slide01

Barka Da Zuwa

TAFKI: Ya kunshi sinadarin hana daukan juna biyu
TASHA: Inda Allurar ta hadu da tafki.
RATA: Fili tsakanin tasha da Allura.
GARKUWAR ALLURA: Ta rufe gajiruwar Allurar (da ta kasa santimita 1)

slide02-a

Amfani da sayana press da kanki
yanada sauki

Mataki uku ne kawai na amfani da sayana press a gida.
Sayana press na hana daukan juna biyu ma wata uku.

slide04

Abu mai sauki kuma zaki iya bayarwa da kanki
don kare kanki daga daukan juna biyu
a tsawon wata uku.


Mace zata iya baiwa kanta wannan samforin a gida ko
tare da taimakon kawarta ko yar uwarta.

slide04

Tana aiki ne don hana daukar juna biyu na
tsawon wata uku bayan anyi Allurar.

Ana bukatar Allurar ne sau daya a kowane wata uku .

GAME DA SAYANA PRESS

Sayana press abu ne mai saukin amfani na sanadarin tsara iyali mafi zabi ga mata.Alura ce mai karamin kai wadda mata za su iya bai wa kansu dan kar su dauki juna biyu na tsawon wata uku.Macen da za ta yi amfani da sayana press ana bukatar ta dauki alurr ko wane wata uku,wanda zai kasance gabadaya sau hudu ah cikin shekara.Mace za ta iya bai wa kanta wannan alurar a gida ko kuma kawarta ta bata,ko yar uwarta a cikin dangin ta.Wannan shafin yanar gizo ya yi bayannin yanda za ayi wannan,ya kuma amsa mafi yawan tambayoyi.

Sayana press yana hana daukan juna biyu ne kawai.

Don kariyar kanka da ga daukar cuta da ake dauka ta hanyar jama’i missali ciwon kanjamau.To kiyi amfani da kwaroron roba.

MEYASA SAYANA PRESS YA ZAMA NA MUSAMAN?

Sayana press alura ce da ake yi a tsakiyar tsoka don hana daukar juna biyu.Alurar takan shiga tsarkiyar shimfida tsoka ta jiki sosai.Mafi yawancin sauran alurai sukan shigaa tsoka ne sosai.Alurar sayana press tana da kankanta kuma gajeruwa ce fiye da alura da aka sani,shiyasa mafi yawan mata sukan ji ciwo kadan ne koh kuma basaji a locacin da ake bayar da alura.

Alura takan fito ne tare da maganin ta a cikin kawai sai dai a bayar.

Sayana press alura ce da wasu kasace suka amince mutun ya bai wa kan shi koda a gida ne.Wasu kasashe suna nazari a kan bukatar mutun ya bayar wa kansa alura sayana press koda a gida kuma ana kyautata zaton za a amince da wannan bukatar.Mutun yayiwa kan shi alura koda a gida ne gabaya bayada wata illa amma akwai wasu abubuwa masu mahinmanci da ya kamata a sani.

Alura nada guntu hudu:

  • Karamin zagayayen tafki.Wanda ya kunshi sinadarin hana juna biyu.

  • ”Tasha”,wanda itace ta hada allurar da ta tafki.

  • Alura da ke wannan na’urar gajeruwa ce(tsawon uku bisa takwas kadai,kasa da centimita daya)

  • Sai marfin alura(da ake kira garkuwa)

Sayana press ta zo cikin karamin murabain jaka ne wanda ke da saukin ajeyewa,sannan kuma a aje wuri mai kariya wanda yara ba zasu taba ba ko dabbobi.Za ayi amfani da sayana press sau daya kachal Kamar yanda aka nuna a bidio sannan a yarda inda ya kamata bayan an kare amfanni.Hanyoyin da za a bi na zubar da sayana press bayan amfani da shi.An yi bayani su a cikin sashe na FAQ amma ka tattauna tare da mutumin da yabaka sayana press akan hanya mafi cancan ta da za’a zubar da shi cikin kariya bayan an kare amfani.

Yawaita Tambaya

Komai game da sayana press

Don neman karin bayani game da Allurar sayana press, Don Allah ziyarci shafin mu na tambayoyi da ake yawan tambaya.

Wasu nau’in na hana daukan Ciki

Sayana press zabi daya ne kacal cikin magunguna na hana daukar juna biyu.Muna karfafawa da kisan sauran.
Hanya daya ta karin samun bayanai itache

bedsider-logo

https://bedsider.org