A wannan sashi zaki sami amsoshin tambayoyi da ake yawan tambaya game da sayana press.Danna kan tambaya don kiga amsa.

Jeren tambayoyi da ake yawan tambaya.

Sau daya ko wane wata uku(mako goma sha biyu zuwa sha hudu). Ki rubuta ranar da ki ka dauki allurar don ki rika tunawa a saukake.

img-faq2
  • Za’a bayarda sayana press ga ciki(tumbi),kogaban saman cinya. Ki nisanci kasan cikin ki ko tabo ko wurin da keda kashi.
  • Ki tabbatar kinyi alurar a sabon bagare a ko wane lokaci da kiyi allurar.

Eh, in har baki iyar bayar wa da kanki , to ki nemi kawarki ko yar uwarki ta yi miki allurar. Kamin allurar, su karanta wannan shafin yanar gizo,su kalli bidiyo,kumma su sami natsuwa wurin aikata wannan matakin.

Illolin sayana press ya kamata ya daina tsakanin sati 15-52 bayan daukar Allurar karshe.

Sauran jaka saya press ya kamata a ajiye shi a yanayin sanyin daki. Kar ki ajiye alurar sayana press a cikin na’urar sanyi kuma ki nisantar ta ita da ga zafi, harma da hasken rana.

  1. Da farko,ki bincika ranar da zata kare amfani a jakar ta. In har ranar yau ta kasance bayan ranar da alarur zata kare amfani ne, to kar kiyi amfani da ita.
  2. Na biyu,duba ruwan allurar a cikin tafkin alurar in kin bude jakar. Bayan kin girgiza magani ya kamata yayi fari-fari.

Ingancin sayana press yafi kashi tis’in da tara (99%) in har anyi amfani da ita yanda ya kamata. Tana da sinadari iri daya da alurar Depo-provera kuma tana hana daukar juna biyu na tsawon wata uku. Mata wadanda basu riga suka samu juna biyu ba,su kadai zasu iya kare kansu daga daukar juna biyu.

Shafin yanar gizo na Pfizer yayi bayani na fasaha game da sayana press har da ingancin ta.

Wasu mata suna samun illoli kadan kuma zaki iya karanta su anan.

Mafi ya wancin illolin abune mai sauki a magance su wasu kuma sukan daina watanni kadan bayan an dauki alurar karshe.

Ya danganta da tsawon lokaci da kin ka dauka kina yi alurar sayana press,jikin ki yana bukatar lokaci don ya ciri sina dari daga tsarin jikin ki.

Ko da yake wasu mata sukan samu zubar jinin al’ada maiyawa lokacin da suke amfani da alurar sayana press,mafi yawanci sukan samu zubar jini kadan ne,ko digar jini tsakani jinin al’ada,ko jinnin al’adar ya tsaya.Wanan illar zata daina da zarar kin bar amfani da sayana press.

Duba shafin illoli don Karin bayani.

Ko wane kaso da’a ka bayar yana hana kwan haihuwar mace ya fito daga gidan kwai(fitar kwai).Alurar sayana press bata lalata juna biyu in har akwai shi..

Sayana press bata zubar da ciki kuma kar kiyi amfani da ita don wanan manufa.

Sayana press ta kunshi milligram dari da hudu na depot medroxyprojesterone acetate,wanda yake shi progestin ne.

Wanan wani kaso ne kadan daga sinadarin da aka yi amfani da shi don hana haihuwa na alurar da ake kira depo provera.

  1. Farko ki tabbata baki da ciki tare da yin gwaji na ciki
  2. Izan ba ki da juna biyu,ki daukar aluran Sayana Press
  3. Kiyi amfani da abun da zai tunatar da ke nan gaba don kar ki manta nan gaba

Kudin da za ki baiya ya bambanta a kowace kasa,amma in kina zaune a Afrika ko Asiya,to sayana press zai kasance dala daya zuwa dala biyu a kowa ne kason alurar da zaki dauka

Jinin al’adar ki zai dawo dadai cikin sati goma sha biyar zuwa hamsin da biyu(wata hudu zuwa shekera daya) bayan kin dauki alurar sayana press ta karshe,ya danganta da tsawon lokacin da kika yi kina daukar alurar.

Fiye da kashi tamanin na mata sukan sami juna biyu a cikin shekar farko da suka bar amfani da alurar sayana press.Sayana press bata hana haifuwa,yana da kyau ki bincika wasu dalillai da suka kawo miki tsaiko na samun juna biyu in har kin shekara daya baki samu juna biyu ba

If you are breastfeeding, you can start using Sayana Press once your baby is 6 weeks or older. SayanaPresswill not preventbreastmilkfromflowing.

– In baki shayar wa, to zaki iya fara amfani da sayana press kwana biyar bayan haifuwa.Jinin al’adar ki zai iya zuba sosai ko ma ya dade fiye da yanda kika saba yi na yan watanni.

Kungiyoyi dayawa sun dukafa warin ganin cewa sayana press ta samu a ko ina a fadin dun iya.

Ba muda cikakken tsarin sunaye amma in har za ki shiga shafen mu na easy@injectsayanapress.org zamu iya gaya miki in har akwai sayana press a kasar ku.

Kungiyar mutane da suka sadaukar da kan su don tabbatar da samuwan hidiman samun iyali da bayani.Ki kara sanin mu a nan.

Ki yi hankuri ki shiga shafen mu na yanar gizo easy@injectsayanapress.org ki gaya mana abun da kike son gani a cikin wannan shafin na yanan gizo.

Za ki iya kuma ziyarta haryan da mukayi amfani da ita wurin gina wannan shafin na yanar gizo don Karin bayani

  • Ki tarbata ba kida juna biyu kafin ki fara amfani da sayana press
  • Zaki iya amfani da alurar sayana press a kowane lokaci na wata.Inkin fara a cikin kwana biyar na farko da fara jinin al’ada (ranar farko itace ranar farko ta jinin al’ada),da ganan sayana press zata fara aiki nan da nan.
  • In kin fara amfani da alurar sayana press a kowane lokaci na wata,ki tabbatar da baki da juna biyu kamin ki dauki alurar farko.Kiyi amfani da wani abu na kariya kwana bakwai mazu zuwa.Bayan kwana bakwai zaki samu kariya daga sayana press.

Mata wa danda:

  • Dama suna da juna biyu,
  • suna da matsanancin ciwo hawan jini ko kuma wa danda suka sami ciwon bugun zuciya
  • matsanancin ciwon kai
  • kuma zubar jinni da baa san dalilin sa ba
  • matsanancin ciwon hanta, da ciwon sugar wanda ba’a iya maganin shi ba,
    lupus (wato matsalar rashin sinadarin garkuwar jiki da wanda keda ciwon sankara, ko wanda ake tuhumar yana da sankara
  • kuma da masu shayar da yaro nono kasa da sati shida

In an bayar da alurar cikin kwana biyar da fara jinin al’ada(ranan farko itace ranar da kika fara jinin al’ada),ita kuma allurar sayana press zata fara aiki nan danan.

Amma in an bayar a kowane lokaci da ba lokacin jinin al’ada ba to ki tabbatar da bakida juna biyu kamin allurar tare da amfani da wani abu na kariya zuwa kwana bakwai.

Bayan kwana bakwai,kin riga ko kin samu kariyar daukar juna biyu daga sayana press.

Eh. Ba damuwa in kin sauya daga alurar Depo-provera zuwa sayana press. Sayana press karamin kaso ne daga Depo-provera kuma yanada kyau tsawon wata uku.

Kiyi amfani da jadawali daya da kike amfani dashi da Depo-provera.

  • Ki mayar da garkuwa akan alurar. Ki jefa gabadayan alurar a cikin inda ake sa abu mai kaifi, ko roba mai kauri ko bokati mai murfi
  • Karki yarda wani mutun ya taba alurar da aka kare amfani da ita.
  • Ki nisantar da bokatin daga yara da dabbobi.
  • Kiyi magana da mutumen da ya baki sayana press dan shawarwari.