Duk da cewa wasu mutane sunyi amfani da alurar sayana press kuma ba wasu illoli,duk da haka yana da kyau ki san illolin da zasu iya faruwa don ki fahimce su ki kuma shirya ma zuwansu. illolin da sayana press ke iya haifarwa kusan daya ne da na sauran sanadaran tsarin iyali.

Common birth control side effects available at bedsider.org

Mafi yawan illolin gasu nan an jera a kasa.

Jinin al’ada ba bisa qa’ida ba:

wasu mata suna yin jinin al’ada ba bisa qa’ida ba,kamar jinin ya rika wasa a lokacin al’adar mace,ko ya zuba da yawa ko kuma ya zuba kadan.Wanan matsalar zata daina in mace ta dauki allurar sau biyu zuwa uku.Mafi yawancin mata jinin al’ada zai iya tsaya masu da ga bisani.Faruwar haka gaba dayanshi daidai ne,kuma baida damuwa kuma baya nufin mace nada juna biyu.Bayan da kika dena amfani da allurar sayana press jinan al’adar ki zai dawo daidai watanni kalilan bayan daukan allurar karshe.

Sauyin nauyi

wasu suna ce wa sun kara nauyi ko sun rage nauyi kwatankwacin kilo biyu da digo biyu lokacin da suke amfani da sayana press. Kiyaye cin abinci mai gina jiki da kuma yanayin rayuwa ta kwarai zasu taimaka wurin rage Karin nauyin.

Ciwon kai

wasu mata sukan sami ciwon kai,amma zaki iya magance damuwar kamar kowane ciwon kai.Kiyi kokari kiyi amfani da maganin kashe zafin ciwo kamar paracetamol,ci abinci da koma shan ruwa sosai ki gani ko zai taimaka.

Inda aka bayar da allurar

zaki iya jin zafi ko karfi wurinda aka bayar da allurar.Kar ki goge wurin allurar.Zafin zai kare cikin kwana biyu zuwa uku.

FAQ

In kina da tambaya, binciki sashen mu na FAQ a nan.