Matakai kadan masu sauki

Amfani da sayana press da kanki yana da sauki.

A kasa mun baki matakai shida na amfani da sayana press.Za ki iya amfani da sayana press da kanki koda a gida ne ko kice kawar ki ta taimaka miki ko yar uwarki.Duk kansu hanya mai sauki ne.

Muna baki shawara da ki kalli bidio don kari akan bayanai dake kasa.


Kalli wannan bidio don ki koyi yanda zaki bayarda Allurar sayana press.

Mataki na farko:Ki zaba kuma ki shirya inda za ki bayar da alurar.

Ki zabi bangare a jikin kin don alurar –Ya kasance tumbin ki yayi nisa da karkashin cikin ki(cibi) ko gaban saman cinyar ki,ki kiyaye da kashi da kuma bangaren da ke da tabo a jikin ki.Farin bangaren da ke cikin hoto zai nuna maki yanda za ki baiwa kanki alurar

Duk wanda zai bayar da allurar sayyana press ya tabata ya wanke hannun shi ko hannun ki da sabulu da ruwa sai ki goge bangaren jikin ki da za ki bayar da alurar.An fi so kiyi amfanni da auduga ko tsumma jikakke mai tsabta, ko kuma giyar goge jiki don alura.In har baki da giyar giyar jiki don alura,to kiya amfani da sabulu da ruwa ya isa.Ki bari wurin da kika goge ya bushe tukunna (kar ki yi amfani da tawul don share wurin).

img-step-1

Mataki na biyu:Ki shirya maganin.

Ki tabbatar da kina da jakar sayana press ajiye,wadda bata da wata matsala.Ki binchika jakar sayana press ki tabbata bata kare aiki ba.Kuma tana cikin yanayin sanyin daki da yakamata.

Ki bude jakar sayana press ki fito da alurar.Ki duba ta da kyau,ki tabbatar cewa alura na da garkuwa akan ta,kuma maganin baya yoyo da ga tafkin.Kuma yakamata akwai tazara tsakanin garkuwar alurar da tashar.In har alurar bata da garkuwa ko tazara,koh in akwai damuwa wurin tafkin,to kijefar da sayana press dinki ki dauko sabo.

img-step-2b

Mataki na uku:Yanda za a hada maganin

Ki rike na’urar ta gefen tasha sai ki girgiza shi sosai tsawon dakika talatin ruwan zai yi kamar fari fari.In ruwan da ke cikin tafkinbai hadu da kyau ba,to ki jefar da sayana press din ki dauko wani

img-step-3B

Mataki na hudu:Ki shirya alurar

Ki rike abun tura alurar da kyau ta gefen tasha da hanu daya,sannan ki rike garkuwar alurar da dayan hannu,sai ki tura garkuwar alurar sama zuwa tasha dan rufe tazarar.Ya kamata kiji sassaukar kara mai kama da karar rufe alkalami da marfin shi.

Da zarar kin rufe tazarar,sai ki cire garkuwar alurar.Yanzu kin hada alurar sai ki rike alurar tana fuskantan sama don kar ta tsiyaye.

img-step-4b

Mataki na biyar:Bayar da kashin alurar

Da hannu daya,tsungula ko ja bangaren jikin ki ta inda za ki bayar da alurar sayana press da dayan hannun,ki rike tashan abin alurar sai ki cusa alurar cikin fatar da kika tsungula ta gefen kasa har sai tashar alurar ta tabi jikin gaba daya.

Abu nagaba shine,ki danna tafkin alurar da kayu tsakanin babban yatsa da manumin ki.Ki matse tafki da karfi ahanakali don tura maganin.Wanan zai dauki kamar dakika biyar zuwa bakwai mai yi yuwa ne ki ga sauran ruwan maganin a cikin tafkin yayin da tafkin ya rushe wannan kuma daidaine.

Bayan daukar kashin alurar,ahanakali kija alurar wajen fatar jikin ki,ki kuma sake fatar da kika tsungula.Za ki iya danne bagaren da aka yi alura da auduga ko tsumma mai tsabta amma kar ki shafa ko goga gurin

img-step-5b

Mataki na shida:Yanda za’a zubar da sayana press da aka yi amfani.

Ki zuba sayana press da aka kare amfani da shi cikin bokiti mai marfi ko gora ko kwalba mai fadin baki mai marfi.Kar a ajiye kusa da yaro ko dabbobi kuma kar a bari wasu mutane su taba da alurar.Ki jefar da bokitin tare da umurni ma’aikacin kiwon lafiya da yabaki sayana press ko kibi ka’idojin zubar da abubuwan da ke da kaifi ko alura.

img-step-6b

*In har kina shakku ko kin bada alurar yanda ya kamata ko baki bayar ba,to ki tunbi ma’aikacin kiwon lafiya da yabaki alura sayana press.Kar ki kara yin wata alura a lokacin,amma ki tabata kin yi amfani da wani nau’i na sinadarin tsarin iyali har locacin da za ki kara daukar wata alurar wato makonni goma sha biyu zuwa sha hudu.
FAQ

Kinada wasu tambayoyi?

Ziyarci sashen mu na FAQ don samun karin bayani game da sayana press.